YANZU YANZU: An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya

YANZU YANZU: An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya

An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai dake jihar Kano, wato Honarabul Garba Durbunde.

NAIJ.com ta samu labarin cewa dan majalisan ya baro Abuja zuwa Kano ne da misalin karfe biyar na yammacin jiya Talata, 30 ga watan Mayu amma sai masu garkuwa da shi din suka tare shi a daidai Jere.

Majiyar ta kara da cewa shi kadai ne a cikin motar a yayin da aka yi garkuwa da shi.

KU KARANTA KUMA: Jihar Sakkawato ta ɗauki nauyin mata 200 domin koyan likitanci

YANZU YANZU: An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya

An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai dake jihar Kano

A halin da ake ciki, Abdulrazak Namdas, kakakin dan majalisar ya yi ikirarin cewa ba shi da masaniya kan faruwar al’amarin. “Bani da masaniya a kan wannan amma an fada mani cewa wasu takardu na dauke da hakan.” Ya fada ma jaridar Premium Times.

Wasu takwarorinsa guda biyu da aka ji ta bakinsu kan lamarin, sun tabbatar da aukuwar hakan, amma suna kan bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An mika 'yan matan Chibok 82 ga gwamnatin tarayya:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel