Anyi ram da ma’aikaciyar asibitin da ta sauya sabon jariri da matacce a jihar Ogun (Bidiyo)

Anyi ram da ma’aikaciyar asibitin da ta sauya sabon jariri da matacce a jihar Ogun (Bidiyo)

Jami’an yan sandan jihar Ogun ta dake wata ma’aikaciyar asibiti da ta sauya sabon jariri da wani gawan jariri ta baiwa mahaifiyar.

Game da cewan wani marubuci Instagram, Adeyemi Abolore, wanda ya daura bidiyon a yanar gizo, wannan abu ya faru ne a karamar hukumar Ifo, jihar Ogun.

Yace ma’aikaciyar asibitin ta gudu da sabon jaririn ana ciro shi sannan ta dawo da wani gawa da sunan cewa ai jaririn ya mutu.

Abolore yace, “ Iyalin wani abokin ta haihu misalin karfe 5 na yammacin ranan 27 ga watan MAyu kuma an cewa sirikarta ta je gida dauko kayayyaki.

Anyi ram da ma’aikaciyar asibitin da ta sauya sabon jariri da matacce a jihar Ogun (Bidiyo)

Anyi ram da ma’aikaciyar asibitin da ta sauya sabon jariri da matacce a jihar Ogun (Bidiyo)

“Da ta dawo, sai aka fada mata ma’aikatan asibitin sun bar asibitin bayan haihuwar. Kuma sauran ma’aikatan basu fadi inda sabon jaririn yake ba. kawai sai mijin ya bude wuta kuma ya kai kara hukuma.

“Sai suka duba inda aka haifi jaririn amma mahaifa kawai aka gani a wurin kuma an rufe dayan dakin. Anyi magana da ma’aikaciyar asibitn misalin karfe 10 na dare kuma ta tabbatar da cewa lafiya jaririn kalau.

KU KARANTA: Anyi garkuwa da dan majalisar wakilai a hanyar Abuja

“Sai yan sanda suka bar asibitin misalin karfe 11:30 na dare tunda matar taki zuwa. Da safe sai aka dawo tana nan, sai muka duba dakin, kawai sai ga jariri a mace kuma tayi ikirarin cewa ai can dama yana dakin.

“Tace ai tun lokacin da aka haifi jaririn yam utu. Dakin da ke rufe da, sai aka ga kudade iri-ri a ciki.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel