Sigari na hallaka mutane miliyan 6 masu busawa a duk shekara

Sigari na hallaka mutane miliyan 6 masu busawa a duk shekara

- Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan 7 taba sigari ke hallakawa a kowacce shekara

- Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana kashe dala biliyan 400 don kulawa da mashaya taba

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan 7 taba sigari ke hallakawa a kowacce shekara, bayan asarar kudin da ya kai kusan Triliyon 1.5, inji rahoton gidan rediyon Faransa.

Shugabar hukumar kiwon lafiya na majalisar, mai barin gado, Margareth Chan ta bayyana haka ne yayin da ake bikin ranar yaki da shan sigari, Chan tace bayan illar da taba ke yiwa masu shan ta, sa’annan tana yiwa muhalli illa sosai ta hanyar hayakin da take fitarwa.

KU KARANTA: Duk gwamnonin Najeriya kakaf babu kamar Bindow – Inji Atiku

Chan ta kara da fadin sigari na haifar da talauci da kuma jefa jama’a cikin halin kunci, bincike ya nuna cewar zukar taba sigari ya sa duniya yin asarar kudin da ya kai kusan dala triliyan daya da rabi wajen kulawa da lafiyar masu shanta.

Sigari na hallaka mutane miliyan 6 masu busawa a duk shekara

Sigari

A wani labarin kuma, majiyar NAIJ.com ta ruwaito masana daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma cibiyar yaki da cutar kansa ta Amurka sun ce sigari na lashe kashi biyu na tattalin arzikin duniya.

Binciken ya nuna cewar akalla dala biliyan 422 ake amfani da su wajen kula da lafiyar masu z-ukar tabar a asibitoci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yakin basasan Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel