Jihar Sakkawato ta ɗauki nauyin mata 200 domin koyan likitanci

Jihar Sakkawato ta ɗauki nauyin mata 200 domin koyan likitanci

- Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal yace gwamnatinsa ta kammala shirin tallafa ma mata 200 domin karatu

- Tattaunawa tayi nisa da jami’ar kasar India domin aikawa da matasan mu su 100, yawancinsu mata

Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal yace gwamnatinsa ta kammala shirye shiryen turawa da mata 200 yan asalin jihar kasar Indiya da wasu kasashe domin yin karatun likitanci.

Tambuwal, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito ya bayyana haka ne a ranar murnan dimukradiyya, 29 ga watan Mayu, inda yace sun mayar da hankali ne akan mata.

KU KARANTA: Duk gwamnonin Najeriya kakaf babu kamar Bindow – Inji Atiku

“Tattaunawa tayi nisa da jami’ar kasar India domin aikawa da matasan mu su 100, yawancinsu mata domin samun horo a fannin karatun likitanci, munyi hakan ne domin kara yawan likitoci mata a jihar.” Inji Tambuwal.

Jihar Sakkawato ta ɗauki nauyin mata 200 domin koyan likitanci

Tambuwal

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito gwamna Tambuwal yana fadin “Mun fara tattaunawa da wasu jami’o’i dake kasar waje don aikawa da matasan mu su 100 da zasu karanci fannonin da suka shafi kiwon lafiya.”

Tambuwal yace gwamantinsa ta shirya wannan tsari ne domin inganta ilimi a jihar ta Sakkwato, inda ya shawarci sauran jama’an jihar da su dage wajen neman ingantaccen ilimi duk da halin rashin kudi da ake ciki.

Daga karshe gwamna Tambuwal yace “Mun dauki wannan mataki ne duk a kokarin gwamnatin jihar wajen ganin ta inganta sha’anin kiwon lafiya a jihar.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Maman Taraba ta amshi yan matan Chibok

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel