Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike kan harbin dalibai

Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike kan harbin dalibai

Muryar Amurka ta bada rahoton cewa gwamnatin jihar bauchi ta kafa kwamiti mai wakilai goma domin ya binciki ummul haba’isin rikicin da ya faru a kwalejin ilimi dake garin kangere daya janyo rufe kwalejin da kuma jikkata dalibai 9 sanadiyar harbinsu da ake zargin sojoji sunyi.

Kwamitin binciken zai gano irin rawar da mutane dai-daiku ko kuma kungiyar mutane suka taka wajen haddasa rikicin, da kuma duba duk wani abu da zai taimaka masa don tafiyar da aikin binciken da kuma sanya duk mutumin da zai taimaka ma kwamitin gudanar da aikinsa.

An baiwa kwamitin wa’adin mako guda don gabatar da rahotonsa dangane da lamarin da ya faru tsakanin sojoji da daliban kwalejin.

Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike kan harbin dalibai

Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike kan harbin dalibai

Da yake jawabi a taron manema labarai da kungiyar daliban ta gudanar, Comrade Shehu Shetima Umar, shine mataimakin kungiyar ta kasa, kuma shine ya jagoranci taron inda ya bayyana cewa lallai sojoji ne suka harbi wadannan dalibai guda Tara, kuma ya bayyana cewa suna shaida daga asibiti da hotuna dake tabbatar da harbin daliban aka yi.

KU KARANTA: Kudin hajji tayi tahi gwauron zabo bana

Dan haka mataimakin shugaban daliban ya bayyana cewa suna bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakinsa farfesa Osinbajo, da mai girma gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi, da shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, su kafa kwamitin da zai binciki lamarin.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Bauchi, Sufurtanda Yusuf Muhammed, ya tabbatar da afkuwar lamarin, shi ma a natshi bangaren mataimakin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, ya bayyana cewa an jawo hanaklin sojojin da ke aiki kusa da kwalejin cewa akwai yamutsi a wurin dan haka ana bukatar kasancewar su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel