Dino Melaye ya baiwa alkalin kotun zabe cin hanci – Sahara Reporters

Dino Melaye ya baiwa alkalin kotun zabe cin hanci – Sahara Reporters

Jaridar Sahara Reporters ta bada rahoton cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisan dattawan tarayya, Dino Melaye, ya biya alkalin kotun zabe, Justice Akon Ikpeme, cin hanci a shari’ar zaben 2015.

A wata maganar rediyo na tattaunawa wayan tarho tsakanin alkalin da Melaye, ana jin tana fada masa cewa ya biya cin hancin a dalar Amurka.

Game da rediyon, Jastis Ikpeme ta bukaci Melaye ya taimaka wata diyarta da aiki a ma’aikatar lafiyan jihar Cross River.

A yayin tattaunawa, Melaye yace ai tuni yayi magana da gwamnan jihar, Farfesa Ben Ayade, akan aikin da ake nema.

Dino Melaye ya baiwa alkalin kotun zabe cin hanci – Sahara Reporters

Dino Melaye

Jastis Ikpeme a shekarar 2016 tayi watsi da karar abokin adawan Melaye, Smart Adeyemi, a zaben sanatan yankin.

Karanta tattaunawar su :

Melaye: Hello,

Justice Ikpeme: Hello

Melaye: Ranki shi dade, yanzu muka fito daga chambers

KU KARANTA: Kudin hajji yayi tashin gwauron zabo

Justice Ikpeme: ina son in sanar da kai cewa na gamsu

Melaye: Yauwa, yauwa, yauwa, yauwa. Zamuje ingila da daren nan. Zan tafi tare da shugaban majalisa ne amma zamu dawo ranan Litinin.

Justice Ikpeme: Okay

Melaye: Saboda haka zamu samu lokaci a mako domin cigaba da magana da ke, idan na dawo, zan zo.

Justice Ikpeme: Ina son in fada maka cewa duk abinda zakayi ka biya a dalar Amurka

Melaye: Ai dama, ba matsala. Ya yar uwata, na baiwa sakataren din-din-din, zasu kirata.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel