Duk gwamnonin Najeriya kakaf babu kamar Bindow – Inji Atiku

Duk gwamnonin Najeriya kakaf babu kamar Bindow – Inji Atiku

- Alhaji Atiku Abubakar ya yaba da aikin gwamnan jihar Adamawa Umar Bindow Jibrilla

- Atiku yace tun bayan kafuwar jihar Adamawa, ba’a taba samun gwamna kamar sa ba

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana farin cikinsa ga yadda gwamnan jihar Adamawa Umar Bindow Jibrilla yake gudanar da aikace aikace a jihar.

Atiku yace tun bayan kafuwar jihar Adamawa, ba’a taba samun gwamnan daya taba kowanne fanni a jihar ba kamar gwamna Bindow, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta samar da attajira da dama ta harkar noma

Atiku ya bayyana haka ne a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a bikin ranar dimukradiyya inda yace gwamnan yayi kokari a bangaren lafiya, Ilimi, lafiya da noma.

Duk gwamnonin Najeriya kakaf babu kamar Bindow – Inji Atiku

Bindow da Atiku

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Atiku yana fadin hakan ne fadar gwamnatin jihar, inda ya kara da cewa, da ace gwmanatocin da suka gabata sun yi irin abinda Bindow yayi, da Adamawa ta zama kamar Abuja.

Daga karshe Atiku yace nasarar da Bindow ya samu baya rasa nasaba da tarbiyyar iyayensa da suka ba shi, sa’annan ya bukaci jama’a su taimaka masa ya zarce a 2019.

“Ina matukar kaunar jihar Adamawa, fiye da kowane waje a Duniya, shi yasa na zuba jari a jihar, kuma zan cigaba da zuba dukiya ta a jihar.” Inji Atiku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Labarin Biyafara, Kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel