Hukumar NDLEA ta kama tabar wiwi mai nauyin kilo 5,863

Hukumar NDLEA ta kama tabar wiwi mai nauyin kilo 5,863

- NDLEA ta cika hannunsu da tarin tabar wiwi mai nauyin kilo 5863 a kan iyakar Seme

- NDLEA tace an shigo da tabar wiwin ne daga kasar Ghana

Jami’an hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA sun cika hannunsu da tarin tabar wiwi mai nauyin kilo 5863 a kan iyakar Seme dake jihar Legas a ranar Talata 30 ga watan Mayu.

NDLEA tace an shigo da tabar wiwin ne daga kasar Ghana, inda aka yi kokarin yin fasa kaurinsa zuwa cikin Najeriya, Inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Yansanda sun gano muggan makamai a makabarta a Kalaba

Cikin wata sanarwa da Kaakakin hukumar, Mitchell Ofoyeju ya fitar yace ta ruwa aka shigo da tabar, inda daga nan aka zuba su cikin wasu motoci guda 2, amma a yanzu sun kama motocin.

Hukumar NDLEA ta kama tabar wiwi mai nauyin kilo 5,863

Hukumar NDLEA

Sa’annan sun kama masu fataucin tabar wiwin, su biyu, cikinsu akwai wani dan Ghana mai suna Adoboe Nana Shelter, sai wani da Najeriya Bola Adigun da wasu yan mata guda biyu, Falilat Sadiq da Mary Ige.

Dayake tsokaci kan kamen, shugaban hukumar, Kanal Muhammad Abdullahi mai murabus ya bayyana kamen a matsayin wani nasara da hukumarsu ke samu a yakin da take yi da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito “Nayi farin cikin kama wadannan kwayoyi, musamman yadda jami’an mu suka yi kwantan bauna suna samame akan masu fataucin tabar wiwin.” Inji Abdullahi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An mika yan matan Chibok ga ma'aikatan mata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel