Fadar shugaban ƙasa tayi watsa watsa da gwamna Fayose, Karanta

Fadar shugaban ƙasa tayi watsa watsa da gwamna Fayose, Karanta

- Babban mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin watsa labaru, Garba Shehu ya mayar da martani ga Fayose

- Muna da tsarin mulki a kasar nan, muna da bangaren dokoki, bangaren shari’a da na zartarwa, Inji Shehu

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin watsa labaru, Garba Shehu, ya bayyana kalaman da gwamna Fayose yayi na cewar shugaba Muhammadu Buhari daya ajiye aiki a matsayin wata hanyar neman suna.

Fayose ya bayyana haka ne a ranar Talata 30 ga watan Mayu, inda yace fadar shugaban kasa bata da nufin mayar da martani ga duk abinda Fayose yace, Shehu yace “Muna da tsarin mulki a kasar nan, muna da bangaren dokoki, bangaren shari’a da na zartarwa.”

KU KARANTA: Idan har da gaske kana son Najeriya to kayi murabus – Inji Fayose ga Buhari

A ranar Talata ne Fayose ya bukaci Buhari da yayi murabus idan dai yana kaunar kasar nan, Fayose yace tunda dai Buhari na ikirarin shi yana yaki da cin hanci da rashawa, toh ba a kwato makudan kudade kadai yaki da rashawa ya tsaya ba, har ma da yin abinda ya dace a lokacin daya dace.

Fadar shugaban ƙasa tayi watsa watsa da gwamna Fayose, Karanta

Fayose

“Zai yi daidai idan yayi murabus, rashin zaman sa a kujerar mulki ya sanya wasu yan kalilan suna tursasa ma yan Najeriya. Don haka muna bukatar shugaban kasa mai karfi a jiki.” Inji shi.

Dayake tsokace kan shekaru 2 na gwamnatin APC, Fayose yace jam’iyyar ta gaza wajen cika alkawurran data dauka gaba daya, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga kalaman Fayose

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel