Rashin Imani: Wata mata da ta kulle 'yar aikin ta har kwana 20 a ban daki

Rashin Imani: Wata mata da ta kulle 'yar aikin ta har kwana 20 a ban daki

- An gurfanar da Oyinyen Chuks, mai shekaru 34,a gaban kotun majistire dake Ikeja a jihar Legas, inda aka tuhume ta da laifin kulle mai aikinta yar shekara 14, a bandaki na tsawon kwanaki ashirin.

- Chuks wacce yar kasuwa ce na zaune ne a namba 19, layin Ojo a unguwar Shasha dake wajen birnin Legas.

Dan sanda mai gabatar da kara Sajan Raphael Donny, ya fadawa kotun cewa an aikata laifin ne tsakanin ranakun 2 zuwa 22 ga watan Mayu a gidan mai laifin.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Donny yace matar da ake zargi da aikata laifin, ta zargi yar aikin da laifin sace mata kudi inda ta lakada mata duka.

”Mai laifin ta kulle yarinyar a cikin bandaki, tana bata abinci sau daya, kana ta hana ta yin wanka ko canja kaya a tsawon kwanakin da ta shafe cikin mawuyacin halin.

“Daya daga cikin makotan matar ce taga baza ta iya cigaba da jure ganin azabtarwar da ake yiwa yarinyar ba, ta sanar da yan sanda, ”yace.

Rashin Imani: Wata mata da ta kulle 'yar aikin ta har kwana 20 a ban daki

Rashin Imani: Wata mata da ta kulle 'yar aikin ta har kwana 20 a ban daki

Dan sanda mai gabatar da kara yace bayan da suka samu rahoton, sun ziyarci gidan inda suka iske yarin cikin mawuyacin hali.

”hakan yasa aka kama mai laifin, yarinyar kuma aka aka kaita asibiti don a duba lafiyarta.”

Laifukan da matar ta aikata sun saba da sashi na 171,203,245 da kuma 285 na kundin manyan laifukan shekarar 2015 na jihar Legas.

Amma kuma Chuks taki amimcewa da dukkanin zarge zargen da ake mata.

Mai Shari’a, uwargida Davies Abegunde ta bada belin matar kan kudi naira miliyan daya tare da mutane biyu daza su tsaya mata.

Ta kuma daga karar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel