An ba matasa dama ta karshe suyi aure ko su hadu da fushin hukuma

An ba matasa dama ta karshe suyi aure ko su hadu da fushin hukuma

- Gwamnatin kasar Burundi ta ce ta baiwa matasan kasar da ke zama tare babu aure da su yi aure nan da karshe shekarar nan ko kuwa su fuskanci biyan tara.

- Shugaban kasar Pierre Nkurunziza shi ya bada wannan umarni da nufin dakile yaduwar rashin tarbiya a kasar.

Ya ce matasan su nuna kauna ga juna da kasar su ta hanyar yin aure.

Ministan cikin gida na kasar Terence Ntahiraja ya ce kasar na fuskantar hauhawan adadin mutane a sakamakon zama da matasa suke tare da juna ba tare da sun yi aure ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa tuni dai wasu suka fara shirya auren mutane da yawa bai dawa domin bin wannan umarni.

An ba matasa dama ta karshe suyi aure ko su hadu da fushin hukuma

An ba matasa dama ta karshe suyi aure ko su hadu da fushin hukuma

Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar na ganin cewa an shiga hakkin mutane idan aka tilasta masu yin aure ba tare da sun shirya ba.

Matasa da yawa dai a kasar Burundi ba su iya biyan kudaden sadakin yin auren.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel