Jiragen ruwa 30 makare da kayan abinci sun iso Legas

Jiragen ruwa 30 makare da kayan abinci sun iso Legas

- Jiragen ruwa 30 ne suka fara isowa Legas makare da man fetur, da sauran kayan abinci

- Har yanzu ba'a fara iso da kaya cikin kasa ba ta river Niger, duk da alkwawurran gwamnati

- Satuttukan nan kayan zasu iso ga jama'a

Da yawa dai daga cikin abubuwan da mutanen Najeriya ke ci har yanzu sai an shigo musu da shi ta ruwa, babu kuma wani katabus da bangarorin yankunan da basu kusa da ruwa zasuyi muddin ba'a shigo da kayan ba an hauro dasu a gingimari.

A sanarwar da hukumar NPA ta fitar, wadda ta rarrabawa manema labarai, ta ce daga yau zuwa 16 ga watan Juni, jirage 30 ne ake tsumayi zasu iso domin jibge kayan amfani a Legas, wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsakar shiga damina, lokutan noma.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Sanda sun gano wani gidan makamai a Benuwe

Jiragen ruwa 30 makare da kayan abinci sun iso Legas

Jiragen ruwa 30 makare da kayan abinci sun iso Legas

Kayayyakin sun hada da gishiri, takin zamani, man fetur, suga, alkama, man ja, bakin mai, da dai sauran kayayyaki.

Idan sun iso, wannan na nufin wadatar kayan musamman a lokacin azumi, da ma zaman farashinsu a kasuwa ba husuma.

A dai baya gwamnatoci sunyi alkawarin yashe ruwan Neja, domin irin wadannan kayayyaki su isa har cikin kasa, zuwa madakata a Baro, ta jihar Neja, don a sami saukin raba su izuwa sauran sassa na arewa mai nisa, amma shiru har yanzu, kamar an manta da lamarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel