Idan har da gaske kana son Najeriya to kayi murabus – Inji Fayose ga Buhari

Idan har da gaske kana son Najeriya to kayi murabus – Inji Fayose ga Buhari

- Gwamnan jihar Ekiti ya kalubalanci shugaba Buhari da ya yi murabus muddin da gaske yake kaunar Najeriya tunda bai da lafiya

- Fayose ya ce zaifi kyautuwa Buhari ya bawa mataimakinsa damar yin aiki yadda yakamata

- Gwamnan ya caccaki jam’iyyar APC cewa ta kasa cika alkawuran da ta dauka lokacin yakin neman zabe

Gwamnan jihar Ekiti Mista Ayodele Fayose ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar muddin da gaske yake kaunar kasar Najeriya to yayi murabus domin bawa mataimakinsa damar yin aiki yadda yakamata tunda bai da lafiya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwanma Fayose ya kara da cewar rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zata taba barin shi yayi aiki yadda yakamata ba.

Da ya juyo ta fuskar auna gwamnatin APC cikin shekaru biyu akan karagar mulki, Fayose ya ayyana cewar gwamnatin Buhari karkashin jam'iyar APC ta kasa cika alkawuran da ta dauka lokacin yakin neman zabe.

Idan har da gaske kana son Najeriya to kayi murabus – Inji Fayose ga Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da yake ban kwana da jami'in gwamnatinsa

KU KARANTA: Wasu ‘yan majalisa 2 sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

Fayose ya kuma soki 'ya'yan jam'iyun adawa da suke sauya sheka zuwa jam'iyar APC da cewar sunayi ne don neman tsira sannan ya kara da cewar yaki da rashawa ya wuce bankado makudan kudaden da ba'asan masu shi ba.

Fayose ya ce: “ganina zaifi kyautuwa ga Buhari yayi murabus maimakon irin wannan tafiyar hawainiya da gomnatin sa takeyi sakamakon rashin sa akan karagar mulki.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce zai kara da shugaba Buhari a zabe 2019. Shin ko wa zai ci nasara tsakanin su. Ku kali bayaninsa a cikin bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel