Daga sama Buhari ke mulki - Femi Fani-Kayode

Daga sama Buhari ke mulki - Femi Fani-Kayode

- Fani Kayode yace Buhari ya fiye yawo

- Tsohon Ministan yace kwanaki 246 Buhari yayi a sama, cikin kwanaki 725 a matsayin shugaban kasa

- A baya dai FFK ya zargi Arewa da kaka-gida da son mulki

A shafin sa na twitter, tsohon minista kuma babban jigo a jam'iyyar PDP, FFK, yace ya kamata Buhari ya farga ya dawo gida domin yayi aiki, ba yayi ta shawagi kasashen duniya ba, inda ya ce, a kwanaki 725 da aka shafe a mulkinsu na APC, kwanaki 246 Buhari yayi yana shawagi a jirgi.

A shafinsa na @real_ffk, ya ce ai ma Buhari ba zama yake ba a Najeriya, baya aiki sai yawo a jirgi.

NAIJ.com ta tattaro cewa a baya ma, Fani-Kayode ya ce yana goyon bayan ballewar Najeriya domin da yawa daga mutanen Arewa basa son na kudu, kuma suna jarabar son mulki.

KU KARANTA KUMA: Ba na adawa da Buhari - Inji Bukola Saraki

Daga sama Buharri ke mulki, inji Femi Fani-Kayode

Daga sama Buharri ke mulki, inji Femi Fani-Kayode

Bisa ga wani rubutu a shafinsa na facebook, FFK yayi wakar tuna wa da kafa kasar Bayafara, wadda ta cika shekaru 50 da kafuwa, ta kuma ruguje bayan shekaru biyu ana yakin basasa a kudancin kasar nan.

A baya NAIJ.com ta kawo cewa Shugaba Buhari dai na can Ingila yana jinya, kuma har iyalinsa Aisha Buhari ta tafi gano shi a asibiti a Landan a jiya Talata, 30 ga watan Mayu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kun goyi bayan juyin mulki a kasar?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel