Wasu ‘yan majalisa 2 sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

Wasu ‘yan majalisa 2 sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

- Wasu ‘yan majalisar wakilan jihar Adamawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki APC

- ‘Yan majalisar sun danganta sauya shekar kan rikicin shugabancin da ya dabaibayi jam’iyyar adawa PDP

- Shugabanin jam’iyar PDP a jihar sun ce su basu damu ba kan sauya shekan ‘yan majalisun biyu

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa wasu ‘yan majalisun wakilai daga jihar Adamawa, batun da ya sake bude wata sabuwar dambarwa a jihar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, cikin ‘yan majalisun da suka sauya sheka suka bar jam’iyar PDP da takaisu kujerar da suke akai, har da dan majalisar wakilai dake wakiltar mazabar Madagali da Michika Mista Adamu Kamale da kuma na majalisar dokokin jihar Mista Emmanuel Tsandu.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan da bikin wankan tsarkin da aka yi musu, Mista Adamu Kamale ya danganta sauya shekar kan rikicin shugabancin da ya dabaibayi jam’iyyar PDP a Najeriya.

Wasu ‘yan majalisu 2 sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

Zauren majalisar jihar Adamawa

To sai dai kuma shugabanin jam’iyar PDP a jihar sun ce su basu damu ba, Alhaji Sabo Garta, dake zama shugaban jam’iyar a yankin Michika ya ce Allah raka taki gona.

KU KARANTA: 'Ba duk nade-naden Buhari ne suka mana dadi ba' -Shugaban APC Oyegun

Shima da yake tsokaci sakataren wani bangare na jam’iyar PDP a jihar Adamawa Hon. Zira Tumba Gaye, ya ce cikinsu bai debi ruwa ba, tun da zama a jam’iyya ra’ayi ne kuma ra’ayi riga ce kowa da yadda yake sa tasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel