Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

- Gwamna Barista M.A Abubakar na jihar Bauchi ya raba wa manoman jihar tan 30,000 na takin zamani don bunkasa harakar noma a jihar

- Wannan gudammawar ne na uku da gwamnan ke rabawa manoman jihar takin zamani

- Gwamnan ya bayyana farashin buhun takin akan naira 5,500

- Gwamnan ya kuma kara da cewa ya ware naira milyan 400 domin horar da manoma a fadin jihar

Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Barista M.A Abubakar ta sake taka muhimmiyar rawar gani a fannin noma. Inda a ranar Talata, 30 ga watan Mayu gwamnan ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman dake fadin jihar, inda aka gudanar da taron rabon takin a karamar hukumar Kirfi.

Idan za a iya tunawa a gudammawar da gwamnatinsa ta baiwa fannin noma a karon farko, gwamnan M.A Abubakar ya raba tan 10,000 a karo na biyu kuma ya raba tan 15,000 yanzu kuma a karo na uku ya raba tan 30,000. Wanda hakan ke nuni da cewa gwamnatin tana baiwa fannin noma muhimmanci.

A yayin da yake jawabi a wurin taron, gwamna M.A Abubakar ya bayyana farashin buhun takin akan naira 5,500. Gwamnan ya kuma bayyanawa dandazon mahalarta taron raba takin cewa gwamnatinsa ta ware makudan kudade domin samar da wadataccen takin zamani a fadin jihar.

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Gwamnan na mika wa wani taki

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin Rariya, gwamnan ya kuma kara da cewa an ware naira milyan 400 domin horar da manoma don ganin sun amfana da shirin bada rancen da aka yi. Haka kuma an raba injinan ban ruwa, maganin kashe kwari da takin zamani ga manoman bayan horar da su.

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Takin zamani da za a rabawa manoma

Daga karshe gwamnan ya shawarci manoman da su yi amfani da kayan da aka ba su ta hanyar da za su amfana kada su banzantar da su.

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Yayin da aka baiwa gwamnan kyautar fatanya

A nasa jawabin, kwamishinan albarkatun gona na jihar Bauchi, Alhaji Yakubu Kirfi, ya yabawa gwamanan kan gudummawar da yake baiwa manoman jihar da kuma yadda yake zuba kudi a harkar noman jihar.

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Gwamnan na gaisawa da wasu mata

KU KARANTA: Siyasa: Matsalolin da Jam’iyyar APC ke fama da su

Kwamishinan ya kuma yabawa gwamnan na amincewa da kai ziyara ga daya daga cikin manyan jami'o'in kasar Morocco domin yin hadaka da jami'ar wajen horar da ma'aikatan ma'aikatar gona na jihar Bauchi tare da tabbatar da karbe ragamar sashen noma na jami'ar Bauchi dake Gadau da kuma Kwalejin noma na jihar.

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Gwamnan na zantawa da manema labarai a wajen taron

Shugaban kungiyar manoma na jihar Bauchi, Barista Haruna Yakubu shi ma ya yabawa gwamnan kan farfado da kamfanin takin zamani na jihar Bauchi.

Gwamnan Bauchi ya raba tan 30,000 na takin zamani ga manoman jihar (Hotuna)

Gwamna Abubakar na ban kwana da jama'a a wajen taron

A yayin rufe taron, an baiwa gwamnan kyautar Kur'ani da dadduma da fatanya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayayyaki na dada karuwa a kasuwanni, ko me yasa haka, ku saurari wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel