EFCC ta kwace wani katafaren gida mallakar dan fadar Jonathan (Hotuna)

EFCC ta kwace wani katafaren gida mallakar dan fadar Jonathan (Hotuna)

- Hukumar EFCC ta kwace wani katafaren gida a Abuja mallakar dan fadar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan zargin rashawa

- Wannan shi ne karo na biyu da hukumar za ta kwace kaddarorin Turnah

- Matasan jihar sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan hukumar ta EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta kwace wani katafaren gida a Abuja dake mallakar George Turnah dan fadar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Hukumar ta wallafa a shafinta ta Fesbuk cewa ta kwace wani gida mai adireshi 2A9 CITEC Estate da ke Abuja.

Wannan shi ne karo na biyu da hukumar EFCC za ta gudanar a kan kaddarorin Turnah kamar yadda ta kwace wasu dukiyoyin sa a Bayelsa.

EFCC ta kwace wani qasaitan gida mallakar yaron gidan Jonathan (Hotuna)

Gidan George Turnah, tsohon mai bada shawara na musamman ga babban daraktan na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) da ke Abuja

NAIJ.com ta ruwaito cewa daya daga cikin kaddarorin da hukumar ta kwace ne wani jib gegen gida da aka sani da 'Kolo Villa' a garin Kolo ta karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa.

EFCC ta kwace wani qasaitan gida mallakar yaron gidan Jonathan (Hotuna)

Adireshin gidan Turnah 2A9 CITEC Estate, Abuja

EFCC ta bayyana cewa, bayan wannan dukiyar da ta kwace, kotu ta kuma ba su umurnin kwace wasu asusun Mista Turnah.

EFCC ta kwace wani qasaitan gida mallakar yaron gidan Jonathan (Hotuna)

Kofar gidan Turnah

KU KARANTA: An zartas da dokar hadin kan kasashe wajen kamo barayin gwamnati a majalisar Dattijai

A halin yanzu, daruruwan matasa a jihar Bayelsa a ranar Talata, 30 ga watan Mayu sun fito don yin zanga-zangar nuna goyon bayan hukumar ta EFCC kan kwace wasu dukiya da kuma tsare Turna wanda shine tsohon mai bada shawara na musamman ga babban daraktan na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).

EFCC ta kwace wani qasaitan gida mallakar yaron gidan Jonathan (Hotuna)

Wajen gidan da EFCC ta kwace

EFCC ta kwace wani qasaitan gida mallakar yaron gidan Jonathan (Hotuna)

Dakin cin abincin gidan Turnah

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel