Ramadan: Ku sa Shugaba Buhari a addu’a-Gwamna Obaseki

Ramadan: Ku sa Shugaba Buhari a addu’a-Gwamna Obaseki

– Gwamnan Jihar Edo ya kira Jama’a su yi wa Shugaban kasa addu’a

– Yanzu haka dai Musulmai na azumi a fadin Duniya

– Shugaban Kasa Buhari na fama da rashin lafiya

Gwamna Godwin Obaseki ya roki Jama’a su yi Shugaba Buhari addu’a cikin azumin nan.

Ana sa ran karba addu’a a cikin wannan wata na Ramadan.

Kuna sane cewa har yanzu babu wanda zai iya cewa ga lafiyar shugaban kasar

Ramadan: Ku sa Shugaba Buhari a addu’a-Gwamna Obaseki

Gwamnan Edo ya nemi Musulman Najeriya su yi wa Shugaba Buhari addu’a

Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo yayi kira ga Musulman Najeriya da su sa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin addu’a yayin da ake azumi a fadin Duniya a cikin wannan wata na Ramadan mai albarka.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai yayi wa Jonathan kakkausan martani

Ramadan: Ku sa Shugaba Buhari a addu’a-Gwamna Obaseki

Wani Gwamna ya nemi ayi wa Shugaba Buhari addu’a

Gwamnan yake cewa dole mutanen Najeriya su kara godewa Allah mai girma ya kuma kira su da cewa ka da su manta da Shugaba Buhari da yake jinya. Gwamna Obaseki yace wannan wata ne na komawa Allah.

Jiya kun samu labari cewa mun fara jin kishin-kishin din cewa Shugaba Buhari ya kusa dawowa Najeriya don ba mamaki ya kamo hanya mako mai zuwa. Daga baya ma dai Uwargidan Shugaban kasar da wuce Landan domin ta ga Mijin na ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sai dai Mutanen Edo sun koka da tashin kaya a Gwamnatin Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel