Yansanda sun gano muggan makamai a makabarta a Kalaba

Yansanda sun gano muggan makamai a makabarta a Kalaba

- Yansandan jihar Kros Ribas sun gano wasu makamai a wata makabarta

- Yansandan sun samu bayanan sirri ne daga wajen wasu jama’a

Kwamishinan yansandan jihar Kros Ribas Hafiz Mohamemd Inuwa ya bayyana gano wasu makamai da jami’an sa suka yi a wata makabarta kusa da jami’ar Kalaba.

Cikin wani hira da kwamishinan yayi da jaridar Daily Trust, ya bayyana cewar sun samu bayanan sirri ne daga wajen wasu jama’a, inda suka aika DPO na yankin, shi kuma ya tabbatar da samun makaman.

KU KARANTA: Badaƙalar naira biliyan 24: An cigaba da cacar baki tsakanin El-Rufai da Jonathan

“Da jami’an mu suka isa makabartar, sai suka hako kabarin da ake zato, nan aka gano bindiga AK 47 guda 5, da alburusa da dama” Inji shi.

Yansanda sun gano muggan makamai a makabarta a Kalaba

Muggan makamai

An gano daya daga cikin bindigar mallakin wani dansanda ne da aka kashe, Sufeto Lawan Onung, dayan kuma a hannun kofur Eeteng Okoi aka kwace, sanadiyyar haka aka sallame shi tun a shekaru hudu da suka gabata.

“Tun bayan da miyagun mutanen suka amshe makaman, sun yi ta amfani dasu wajen aikata ta’addanci akan jama’an garin Kalaba.” Inji Kwamishinan.

Daga karshe majiyar NAIJ.com ta jiyo shi inda ya bada tabbacin rundunarsu zata cigaba da gudanar da bincike domin tabbatar da kamo mutanen da suka ajiye makaman.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Soyayyar Najeriya, Inji Obasanjo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel