Igbo sun tsayar da al'amura don goyon bayan Biafra

Igbo sun tsayar da al'amura don goyon bayan Biafra

- kungiyoyin da ke fafutukar kafa yankin Biyafara sun sayar da al’amura cak a wasu manyan biranen yankin kudu maso gabashin Najeriya

- Kungiyoyin sun sanar cewa mutane su zauna a giadajensu don tunawa da shekara 50 na fara fafutukar kafa yankin Biyafara

- Yawanci shaguna da ke biranen yankin suka kasnace a rufe

Rahotanni daga kudu maso gabashin Najeriya na cewa al'amura sun tsaya cak a wasu manyan biranen yankin don nuna hadin kai kan kiran da kungiyoyin da ke fafutukar kafa yankin Biyafara suka yi na kasancewa a gida.

Kungiyoyin IPOB da MASSOB sun yi wannan kira ne na cewa mutane su zauna a giadajensu a matsayin zanga-zangar lumana, don tunawa da shekara 50 na fara fafutukar kafa yankin Biyafara da marigayi Chukwuemeka Ojukwu ya yi.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, fiye da kashi 90 cikin 100 na shagunan da ke birnin a rufe suke, haka ma babbar kasuwar birnin ta kasance a rufe. Sai dai kuma ana ci gaba da harkokin sufuri.

Igbo sun tsayar da al'amura don goyon bayan Biafra

'Yan kungiyoyin da ke fafutukar kafa yankin Biyafara

Haka ma a birnin Umuahia inda nan ne garin jagoran masu fafutuka na kungiyar IPOB Nmandi Kanu ya fito, yawanci shaguna sun kasnace a rufe amma akwai kadan da suka bude.

A birnin Anacha na jihar Anambra kuwa, harkokin da suka hada da na kasuwanci da sufuri da makarantu da bankuna duk sun kasance a rufe.

KU KARANTA: Toh fa: Kungiyar kabilar Igbo ta yi wa Kanu kashedi

Dukkan sauran jihohin yankin ma ana cikin irin wannan yanayi. Yankin kudu maso gabas dai ya kunshi jihohin Anambra da Enugu da Abia da Imo da kuma Ebonyi.

Zuwa yanzu dai babu wani rahoto na tashin hankali, amma tuni aka jibge jami'an tsaro a muhimman wurare da ke jihohin yankin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A karshe dai Nnamdi Kanu ya samu yanci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel