Gwamnatin Buhari ta samar da attajira da dama ta harkar noma

Gwamnatin Buhari ta samar da attajira da dama ta harkar noma

- Lai Muhammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da sabbin attajirai masu kudi da tsare tsaren data yi ma harkar noma.

- Lai ya kara da cewa an samu nasara a noman hatsi da shinkafa a jihohin Kebbi, Kano, Jigawa, Ebonyi da Sokoto

Ministan watsa labaru da raya al’adun gargajiya Alhaji Lai Muhammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da sabbin attajirai masu kudi da tsare tsaren data yi ma harkar noma.

Lai ya bayyana haka ne a ranar Talata 30 ga watan Mayu yayin wat hira da yayi da gidan talabijin na Channels Tv, inda ya amsa tambayoyi dangane da nasarorin da gwmnatin Buhari ta samu a shekaru 2.

KU KARANTA: Badaƙalar naira biliyan 24: An cigaba da cacar baki tsakanin El-Rufai da Jonathan

Lai yace manoma da dama sun amfana sakamakon tsare tsaren da gwamnatin Buhari tayi musamman a bangaren noma inda babban bankin Najeriya, CBN ke baiwa kananan manoma rance, ita kuma ma’aikatar noma ta basu iri da shawarwari.

Gwamnatin Buhari ta samar da attajira da dama ta harkar noma

Minista Lai

Lai ya kara da cewa an samu nasara a noman hatsi da shinkafa a jihohin Kebbi, Kano, Jigawa, Ebonyi da Sokoto, hakan ya taimaka wajen samun karuwan yawan shinkafar gida a kasuwanni, kuma ya janyo ra’ayin matasa ga noma.

Sai dai ministan yace duk da cewa farashin shinkafar gida yayi tsada, amma ana sa ran zai sauko nan bada dadewa ba zuwa lokacin da za’a fara girbi a kakar badi. Ministan ya ce a yanzu gwamnati ta karya farashin taki daga N9000, zuwa 5000 tun bayan fara samun taki daga kasar Morocco.

Minista Lai yace tattalin arzikin kasar na habbaka kadan kadan idan aka yi duba ga fannin noma dana ma’adanan kasa.

“A lokacin da muka zo gwamnati, yan kwangila na bin mu bashin naira triliyan 1 da biliyan 700, anyi watsi da ginin hanyoyi 202, a shekarar 2015 gaba daya, naira biliyan 18 kacal aka kashe a akan gina hanyoyi,da naira biliyan 5 akan lantarki.

“Amma a shekarar 2016/2017 mun kashe naira triliyan 1 da biliyan 200 akan manyan ayyuka, naira biliyan 260 akan hanyoyi da biliyan 90 akan lantarki. Mun samar da kilomita 320 na sabbin hanyoyi, tare da gyara kilomita 460, mun gina gadajoi 24 tare da gyaran 21. Mun fara aikin gina layin dogo daga Legas zuwa Ibadan.” Inji shi.

NAIJ.com ta ruwaito ministan yana nanata manufar gwamnatinsu na dagewa wajen inganta tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da rashawa, inda ya kara da cewa ba’a san halin da kasar zata shiga ba da Buhari bai ci zabe ba.

“Idan ba’a manta ba mun samu farashin gaggan mai a akan dala 30 ne, yayin da gwamnatin data gabata ta siyar da mai har a dala 100, kuna ba zaku hada samun kudin ba, amma duk da karancin kudin, mun cigaba da tara kudi a asusun gwamnati.” Inji Lai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An mika yan matan Chibok ga Aisha Alhassan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel