'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

- Tsohon Gwamna na Cross-Rivers, Donald Duke na son takarar shugabancin kasa

- Ya taba yin takara shekaru goba da suka wuce a karkashin PDP

- Yana shinshinar takara a 2019

A taron da aka yi a Legas a yau da safen nan, mai taken samari a siyasa, tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Mr. Donald Duke, ya je akwai yiwuwar kara takarar sa, a zabe mai zuwa.

Ya ce akwai yiwuwar a sake ganinsa a fagen siyasar kasar nan, domin shekaru 10 kenan da ya bar siyasa.

KU KARANTA KUMA: 'Yar talakawa ta ci kyautar Naira miliyan 6 a gasar Kimiyya

'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

"Ba sai ka kai shekaru 50 ba ne zaka fara duba rawar da zaka taka', ya kara da cewa. Dole samari su fito a dama dasu.

'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

Ya kuma ce "naki zuwa majalisar dattijai ne don na girmi harkar, shugabancin kasa ne nafi sha'awa, kuma ina duba yiwuwar hakan a nan kusa."

NAIJ.com ta tuna cewa shekarar 2007 dai Mr. Donald Duke ya nemi takarar shugabancin kasar nan, amma aka zabo Goodluck Jonathan daga yankin, aka yi fatali da shi, duk da cewa yafi Jonathan din farin jini da gogewa, da iya mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel