Gwamnati zata raba naira miliyan 100 a Bauchi

Gwamnati zata raba naira miliyan 100 a Bauchi

- Gwamnatin tarayya zata fara bada tallafin kudi a kowane wata ga mutanen jihar Bauchi

- Kamfanin Mobile Money Operatots aka ba amanar biyan kudin zuwa ga wadanda zasu amfana da shirin

- Akalla mutane 10,800 ne zasu amfana daga yankuna 360 na kananan hukumomi 12 a jihar

A ranar Talata, 30 ga watan Mayu ne za'a fara biyan naira 5,000 a wata karkashin wani shirin tallafin kuɗi na gwamnatin tarayya a Bauchi.

Jami'an tabbatar da wannan shiri sun bawa 'mobile money operatots' (MMO) aikin tabbatat da biyan kudin zuwa ga wadanda zasu amfana a garuruwan su. MMO ta bayyana hakan ne bayan wani zama da ta yi da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Bauchi.

Ana sa ran mutane 10,800 ne zasu amfana daga yankuna 360 na kananan hukumomi 12 a jihar ta Bauchi ne zasu amfana inda zasu karbi naira 10,000 kowannen su na watannin disamba da janairun wannan shekara cikin mako mai zuwa.

Gwamnati zata raba naira miliyan 100 a Bauchi

Mutane 10,800 ne zasu amfana daga tallafin kudi naira 5,000 a kowane wata

KU KARANTA: Arewa ta yaba, kudu ta yi Allah wadai da mulkin Shugaba Buhari na shekara 2

Har ila yau, gwamnatin jihar Bauchi tana sanar da 'yan jihar cewa za'a buɗe sashin yanan gizo na N-power ranar 13 ga watan gobe kamar yadda NSIP ta shaida.

Gwamnan jihar M. A Abuabakar zai tabbatar da kyakkyawan alaka tsakanin gwamnatin sa da gwamnatin tarayya sabida amfanin jihar Bauchi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bada takaiceccen shugabancin shugaba Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel