Shekaru 2 da mulki: Ministan Buhari ya daba masa wuka ta baya?

Shekaru 2 da mulki: Ministan Buhari ya daba masa wuka ta baya?

– Ministan kwadago Chris Ngige yayi magana game da Gwamnatin Buhari

– A cewar sa Jama’a da dama ba haka su ka so ba

– Sai dai Ministan yace ko da ba a biya burin Jama’a ba ya gamsu

Ministan kwadago Chris Ngige yace Jama’an kasa da dama ba su gamsu da tafiyar su ba

Sai dai Ministan yace shi fa duk da haka yana jin cewa sun yi kokari

Ministan ya jero irin matsalolin da wannan Gwamnati ta samu

Shekaru 2 da mulki: Ministan Buhari ya daba masa wuka ta baya?

Shugaba Buhari tare da Ministan sa Ngige

Ministan kwadago Sanata Chris Ngige yake cewa da bakin sa Jama’an Najeriya da dama sun yi burin ganin canji fiye da haka daga Gwamnatin su sai dai yace duk da haka shi yana jin cewa wannan Gwamnati tayi matukar kokari.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta wuce Landan domin ta ga Mijin ta

Shekaru 2 da mulki: Ministan Buhari ya daba masa wuka ta baya?

Jama’a da dama ba su gamsu da tafiyar mu ba-Iji wani Minista

Ngige ya bayyana yadda Gwamnatin ta rika samun cikas musamman wajen sha’anin man fetur wanda shi Najeriya ta dogara da shi inda ya karye a kasuwa hakanan kuma Gwamnatin tayi fama da Tsagerun Neja-Delta da suka yi ta ta’asa.

Dazu kun ji cewa Ministan na kwadago Chris Ngige ya soki ‘Yan uwan sa Inyamurai da ke sukar Gwamnatin Shugaba Buhari su na cewa an ware su gefe. Ngige yace a lokacin yakin neman zabe sam Inyamurai ba su taimakawa Buhari ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kudin Najeriya za ta kara daraja kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel