Badaƙalar naira biliyan 24: An cigaba da cacar baki tsakanin El-Rufai da Jonathan

Badaƙalar naira biliyan 24: An cigaba da cacar baki tsakanin El-Rufai da Jonathan

- El-Rufai ya caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan

- Gwamnan ya soki lamirin Jonathan ne kan wasu makudan kudade naira biliyan biyu

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan kan wasu makudan kudade naira biliyan biyu da tsohon shugaba Jonathan ya rabar ma kowanne gwamnan PDP a zamaninsa.

Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Talata 30 ga watan Mayu ta bakin Kaakakin sa Samuel Aruwa, inda yace tsohon shugaban ya kasa bada kwararan hujjoji dangane da dalilin dayasa shi raba ma gwamnonin jam’iyyar PDP kadai makudan biliyoyin nairori.

KU KARANTA: Paul Pogba: Ɗan ƙwallon da yafi riƙo da addinin Musulunci

“Jonathan matsoraci ne, kuma baya ya daukan nauyin ire iren mataken daya dauka a zamaninsa.” Inji El-Rufai. Gwamnan ya cigaba da fadin “A watan Maris na 2015, jim kadan bayan ya taya shugaba Buhari murnan lashe zabe, amma sai ya zagaya ya kira yan koransa yana fada musu kada su yarda da sakamakon zaben.” Kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.

Badaƙalar naira biliyan 24: An cigaba da cacar baki tsakanin El-Rufai da Jonathan

El-Rufai

Majiyar NAIJ.com ta jiyo “Sai dai hakarsu bata cimma ruwa ba, kuma Allah ya daura yan Najeriya akansu, don haka ba’a bin mamaki bane idan ya musa zarginsa da nayi na raba biliyoyin nairori ga abokansa gwamnoni.

“Kowa ya san Jonathan ya tafiyar da gwamnatin Najeriya a zamaninsa ne kamar ta abokai da iyalansa.” Inji gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Gwamnan ya kara da cewa tsohon shugaban Jonathan ya aksa bada kwararan bayanai masi gamsarwa da zasu nuna cewar shi El-Rufai karya yake yi kan zarginsa da yayi, inda yace batun rabon kudi naira biliyan 2 ga kowanne gwamnan jihar PDP a zamaninsa na nan a rubuce cikin rahoton taron majalisar zartarwa.

Daga nan El-Rufai ya gargadi tsohon shugaban kasar da cewa binciken da ake yi yanzu kan batun kudaden ba daga wajen sa bane, don ba shi ya sa ba. Majalisar zartarwa ce ta bada umarnin binciken, don haka ba shi ya kashe zomon ba, rataya aka bashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Batun Obasanjo akan Najeriya

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu
NAIJ.com
Mailfire view pixel