Akawun majalisar dokokin jihar Sakkwato ya rasu

Akawun majalisar dokokin jihar Sakkwato ya rasu

- Suleiman Muhammad Akawun majalisar dokokin jihar Sakkwato, ya rasu

- Aminu Waziri Tambuwal ya samu halartan jana’izar tare da mataimakinsa

Akawun majalisar dokokin jihar Sakkwato, Suleiman Muhammad ya rasu da safiyar ranar Talata 30 ga watan Mayu, kamar yadda majalisar ta sanar.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito Akawun majalisar ya rasu yana da shekara 53, kuma ya rasu ne a wani babban asibitin garin Sakkwato bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

KU KARANTA: Dangantakar dake tskanina da gwamna Tambuwal – Obasanjo

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar tuni an binne Akawun kamar yadda musulunci ya tanada bayan anyi masa jana’iza a masallacin juma’a na sarki Muhammadu Maccido.

Akawun majalisar dokokin jihar Sakkwato ya rasu

Majalisar dokokin jihar Sakkwato

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya samu halartan jana’izar tare da mataimakinsa, Ahmed Aliyu, Kaakakin majalisa Salihu Maidaji da mataimakinsa Abubakar Magaji da dai sauran manyan mutane.

Marigayin ya fara aiki ne da majalisar dokokin jihar a shekarar 2016 bayan yayi murabus daga aikin gwamnati, kuma ya rasu ya bar yara 13 da mata 3.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kana da labarin darajar Naira?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel