Soji na bincikar mutum 1,400 kan zargin ko suna da alaka da Boko Haram

Soji na bincikar mutum 1,400 kan zargin ko suna da alaka da Boko Haram

- Majiyar soji ta Najeriya ta ce tana bincikar sama da mutum 1,400 kan ta'addanci

- A baya ma dai an saki da yawa wadanda ake tuhuma, ciki har da mata da yara

- Yakin da ake da Boko Haram yayi kamari a shekarun baya, yanzu abin ya lafa

A ci gaba da sojin Najeriya keyi, da yaki da ta'addanci, ana bincikar akalla mutum 1,400, a cewar Maj. Gen. Lucky Irabor, a bikin mika ragamar mukaminsa na Theatre Commander, na Operation Lafiya Dole, a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ya mika ragamar ne ga Manjo Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya baro hukumar MNJTF, hadakar kasashe masu yakar Boko Haram ta soji.

KU KARANTA KUMA: Ka ji masu yi da gaske: Dangote zai kashe Dala Biliyan 1 wajen noman shinkafa

A cewar Gen. Irabor, da yawan wadanda ake zargin an kama su ne a fagen daga, wasu kuma sun mika kansu ne domin sun gaji da harkar, ko an jikkata su yayin barin wuta.

Ya kara da cewa, da yawa daga cikinsu, sun tabbatar da kansu cewa su mayakan Boko Haram ne, kuma wasunsu ma sunyi nadama, wasu kuma ana cikin wayar musu da kai domin ciro su daga zazzafan ra'ayi. 'Wasu kuma an mika su gaba domin tuhumar kotu, a cewarsa'.

Yayi kira ga magajin nasa da ya zage damtse kar a koma gidan jiya, ya kuma yi kira ga samario da su guji masu tunzura su, yace ta'addanci baya haifar wa da kowa da-mai-ido.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel