Yan bindiga sun hallaka manoma 3 a jihar Taraba

Yan bindiga sun hallaka manoma 3 a jihar Taraba

- Yan bindiga sun kashe manoma 3 a garin Gassol, na karamar hukumar Gassol dake jihar Taraba

- Yan bindigan sun kai hari ne garin Gassol da cikin dare

Wasu yan bindiga sun kashe manoma su 3 a garin Gassol, na karamar hukumar Gassol dake jihar Taraba, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito yan bindigan sun kai hari ne garin Gassol da cikin dare inda suka bude ma yan garin wuta yayin da suke barci, nan take mutane uku suka ce ga garinku nan, tare da jikkata jama’a da dama.

KU KARANTA: Gidan sama hawa 3 ya ruguje a jihar Legas, rayuwaka da dama sun salwanta

Wani mazaunin garin, Malm Bako Disol ya shaida cewa ba’a san daga inda yan bindigan suka fito ba, amma dai dama garin nasu na fama da yawaitan hare haren yan bindiga a yan kwanakin nan tare da matsalar fashi da makami.

Yan bindiga sun hallaka manoma 3 a jihar Taraba

Yan bindiga

Malam Bako yace jama’an garin nasu sun dauko hayar yan banga domin su dinga tabbatar da tsaro a yankin, toh amma saboda karancin makamai ga yan bangan da kuma karfin miyagun makaman da Yan bindigan ke amfani da shi, an kasa shawo kan hare haren.

“Sakamakon matsalar fashi da makami da na garkuwa da mutane, attajiran yankin sun tattara sun bar Gassol.” Inji shi.

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Gassol, Alhaji Yahuza game da harin, ya tabbatar da lamarin, sa’annan yace sun kira taron shuwagabannin al’ummar tare da masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin gano bakin zaren.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya: Obasanjo ya bada shawara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel