Toh fa: Shettima ya umarni kama duk masu hannu wajen awon gaba da abinci ‘yan gudun hijira

Toh fa: Shettima ya umarni kama duk masu hannu wajen awon gaba da abinci ‘yan gudun hijira

- Gwamnan Jihar Borno ya umarni kama duk masu hannu wajen awon gaba da abinci ‘yan gudun hijira a jihar

- An raba buhun shinkafa guda 2,250 da wasu kayayyakin abinci ga ‘yan gudun hijira da ke makarantan firamare na Lamusila

- Shettima ya ce umarni kama mutanen ya zama dole idon akayi la’akari cewa kashi 50 na kayayyakin abinci ga ‘yan gudun hijira aka karkatar

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Litini, 29 ga watan Mayu ya bada umarnin a kama duk 'yan iskan da yake da hannu wajen karkatar da abinci Ramadan na ‘yan gudun hijirar, a cikin garin Maiduguri da kuma yankin Jere.

Shettima ya bada wannan umarni ga 'yan sandan jihar, yayin da yake rarraba buhun shinkafa guda 2,250, sukari da kuma gongonin tumatir a makarantan firamare na Lamusila.

KU KARANTA: 'Yan gudun hijira za su yi Sallan layya a gida — Shettima

Ya ce wannan umarni ya zama dole ne idon akayi la’akari cewa kashi 50 na kayayyakin da za a rarraba na taimakon abinci ga ‘yan gudun hijira aka kwace ko karkatar da su wanda kuma zai iya kawo tikas ga cibiyoyin da abin ya shafa.

Toh fa: Shettima ya umarni kama duk masu hannu wajen awon gaba da abinci ‘yan gudun hijira

Sansannin ‘yan gudun hijira

NAIJ.com ta ruwaito cewa gwamnan da kansa ya jagoranci raba kayayyakin abinci sama da sa'o'i uku, kafin komawarsa ga fadar gwamnatin jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari bayanai mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan yakin basasa ta Biafra

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel