'Ba duk nade-naden Buhari ne suka mana dadi ba' -Shugaban APC Oyegun

'Ba duk nade-naden Buhari ne suka mana dadi ba' -Shugaban APC Oyegun

- Shugaban jam'iyya ya koka da yadda Buhari yayi nade-naden siyasa

- Ya yaba da irin aikin da suka yi a gwamnatance

- Ana bikin cikarsu shekaru biyu a kan mulki

A yayin da ake bikin cika shekaru biyu da mulkin APC, shugaban jam'iyyar APC Chief John Odigie-Oyegun, ya ce ba duk nade-naden mukamai ne suka farantawa jam'iyyarsa rai ba, ya kuma ce an sami rashin jituwa tsakanin mabiya bayan nade-naden.

A cewarsa: "Dole in fada muku gaskiya, ba kowa ne da yayi wa jam'iyya aiki ya sami yadda yake so ba lokacin bada mukamai, amma kuma akwai lokacin gyara wa."

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu (HOTUNA)

'Ba duk nade-naden Buhari ne suka mana dadi ba' -Shugaban APC Oyegun

'Ba duk nade-naden Buhari ne suka mana dadi ba' -Shugaban APC Oyegun

Ya kuma ce a lokacin da suka hau mulki sun taras da barna da yawa daga PDP, da ma kuma abubuwan da basu hango ba, wadanda suka saka dan jan lokaci kafin a fara gani a kasa.

KU KARANTA KUMA: Ka ji masu yi da gaske: Dangote zai kashe Dala Biliyan 1 wajen noman shinkafa

A karshe NAIJ.com ta kawo inda yace za'a ci ribar shukar da suke yi saboda sabon tsarin da gwamnati ta faro na kyautata rayuwar al'umma.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel