Ko kun san maganin kashe kwayoyin cutar da ka iya ceton rayuka?

Ko kun san maganin kashe kwayoyin cutar da ka iya ceton rayuka?

- Masana kimiyya sun gano wani sabon launin maganin kashe kwayoyin cuta

- Masu binciken sun ce maganin zai inganta yaki da cutuka masu bijirewa magunguna

- Dakta Dale Boger ne ya jagoranci masu nazari

Masana kimiyya sun yi bajintar kirkiro wani sabon launin maganin kashe kwayoyin cuta, da ka iya ceto rayukan dumbin al'umma.

Sun ce binciken zai inganta yakin da suke yi da cutuka masu bijirewa magunguna, daya daga cikin babbar barazana ga lafiyar al'ummar duniya.

Masu bincike sun jirkita rukunin kwayar atom na wani magani mai suna Vancomycin inda karfinsa ya ninka har sau kusan 1,000.

Ko kun san maganin kashe kwayoyin cutar da ka iya ceton rayuka?

Sabon launin maganin kashe kwayoyin cutar da ka iya ceto rayuka dumbin al'umma

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, maganin ka iya far wa kwayar cuta ta fuska uku, abin da zai zame mata mai matuƙar wahala ta samu kuzarin rama faɗa.

KU KARANTA: Dangote zai bude wani makeken kamfanin sukari a Najeriya

Dakta Dale Boger na cibiyar Scripps a California shi ne jagoran masu wannan nazari.

Ya ce: "Sauyin da muka yi masa, zai kasance abu mai wahala kwayar cuta ta iya bijirewa wannan magani."

Alkaluma sun ce irin waɗannan cutuka na haddasa mace-mace kimanin dubu 50 duk shekara a Amurka da Turai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayan masarufi a kasuwannin Najeriya a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel