YANZU YANZU: Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

YANZU YANZU: Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

- Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tafi birnin Landan ganin mijinta

- Zata dauki tsawon wani lokaci tare da maigidanata shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Landan

- Shugaba Buhari na hutu a birnin Landan inda yake ci gaba da jinya

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tafi birnin Landan a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, kwanaki 23 bayan mijinta ya bar kasar domin ci gaba da jinya.

A cikin wani jawabi dauke da hotunan uwargidan shugaba Buhari a lokacin da ta isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, mataimakiyarta ta musamman a kafofin watsa labarai, Adebisi Olumide Ajayi ta ce ta tafi birnin Landan ne domin kasancewa da mijinta na dan wani lokaci.

Jawabin ya zo kamar haka: “Mai girma uwargidan shugaban kasa zata dauki tsawon wani lokaci tare da minjinta shugaba Muhammadu Buhari wanda a yanzu ya ke hutun jinya.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya yi yunkurin kashe kan shi saboda an hana shi takarar shugaban kasa

YANZU YANZU: Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

Uwargidan Buhari na nuna godiyarta ga miliyoyin ‘yan Najeriya dake ta yima maigidanta addu’an samun lafiya da kuma fatan dawowa lafiya.”

YANZU YANZU: Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

NAIJ.com ta tuno cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan don ci gaba da jinya a ranar 7 ga watan Mayu.

Uwargidan shugaban kasa Buhari ta mayar da hankali ga aiki da take kaddamarwa a yankin Arewa maso gabas, don ganin ta tallafa wa mata da sana’oi, karatun yara mata da kuma bayar da cikakken kula ga yan gudun hijira a Arewa maso gabas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kun goyi bayan kuyin mulki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel