Gwamnonin APC na so suyi taron kasa banda Buhari

Gwamnonin APC na so suyi taron kasa banda Buhari

- Janar Buhari dai yana jinya a asibiti.

- Gangamin siyasa na iya kwace ikon jam'iyya ya baiwa wani.

- Shugaban jam'iyya yace dole a jira Buhari ya dawo

A cikin jaddawalin su na cika shekaru biyu a karagar mulki, gwamnonin jam'iyyar APC sun ce zasu mika wa mjukaddashin shugaba Buhari, Farfesa Yemi Osibanjo kalanda, domin ya zaba musu ranar da zasu yi taron kasa, domin ba sai sun tsaya jiran shugaba Buhari ya dawo ba, duk da cewa a al'adance shine jigon tafiyar tasu.

A martanin shugaban jam'iyya dai zuwa yanzu shine, dole a jira shugaba Buhari ya murmure a yi da shi, domin baza ayi babu shi ba.

Ya kara da cewa, duk wanda yake son maganar 2019 kuma, sai jam'iyya ta jira taji ra'ayin zababben shugaban kasa, ko yana son yayi takara ko kuma baya so, sannan a iya baje kolin ga gwamnoni.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

Gwamnonin APC na so suyi taron kasa banda Buhari

Gwamnonin APC na so suyi taron kasa banda Buhari

A al'adance dai, shugaba Buhari shine jigon tafiya, da yawa kuma daga cikin gwamnonin nan sun ci zabe ne a karkashin babbar rigarsa.

NAIJ.com ta tattaro cewa gwamnan da ya bada sanarwar tun asali shine gwamnan plato, Lalong, a wurin taron kuwa akwai gwamnonin APC da yawa, kamar na Binuwai, Katsina, Edo, Bauchi, Niger, da Zamfara, sai mataimakan gwamnonin jihohin Imo, Legas, Kogi, Osun da Ogun.

Ana dai sa rai wani ne zai tsaya takara a karkashin jam'iyyar muddin shugaba Buhari ya yanke shawarar hutawa domin tsufa da karin lafiya, lokutan zabe masu zuwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel