Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu (HOTUNA)

Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu (HOTUNA)

-Yan kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara sun yi ma shugaban k=su kyautar saniya mai suna Buhari.

- Sun bayar da kyautan saniyan ne domin bikin tunawa da ranar Biyafara

- Kungiyar ta umurci magoya bayan ta da su zauna a gida domin kauracewa bikin demokradiyya da kuma yin arangama da jami’an tsaro

Rahotanni sun kawo cewa wasu daga cikin ‘yan kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara dake zaune a kasar Malaysia bayan sun dawo Najeriya sun mika ma shugaban kungiyar ta su Nnamdi Kanu saniya da suka rada ma suna Buhari domin a yi amfani da shi gurin tuna ranar Biyafara

Wannan ya biyo bayan korafin da kungiyar ta yi na umartan magoya bayan ta da su zauna a gida domin kauracewa bikin demokradiyya da kuma yin arangama da jami’an tsaro.

KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba – hukumar shirya gangamin zabe

Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu (HOTUNA)

Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu

Har ila yau a baya NAIJ.com ta ruwaito cewa daruruwan jama’a ciki harda manyan yan siyasa sun ziyarci shugaban kungiyar a gidansa, domin yi masa sannu bayan ya fito daga gidan kurkukun Kuje, sakamakon beli da babban kotun birnin tarayya ta ba sa.

Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu (HOTUNA)

Shugaban kungiyar ta Biayafara, Nnamdi Kanu tare da magoya bayan sa

Rahoton ya kuma labarta cewa tuni ‘yan kungiyar suka lakawa ‘San’ suna Buhari tun kafin su mikawa shugabansu kuma wasu biyu daga cikin ‘yan kungiyar suka yi hoto da ‘San’ da kuma shugaban.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel