Bikin cikar Kano shekara 50 na dada kara armashi

Bikin cikar Kano shekara 50 na dada kara armashi

- Gwamnatin jihar Kano na cigaba da gudanar da bukukuwan cikar Kano shekara 50 da kafuwa inda gwamna Ganduje ya jagoranci tattaunawa tsakanin gwamnati da al’ummar gari

- Gwamnati ta gudanar da liyafa domin karrama yan mazan jiya da suka taka gagarumin rawa wajen kafuwar Kano

- Sauran bukukuwan sun hada da bikin hawan dabar da kuma rangadi a wasu ayyuka gwamnan

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci taro na musamman da aka shirya na tattaunawa tsakanin gwamnati da al’ummar gari a cigaba da bukukuwan cikar Kano shekara 50 da kafuwa.

Gwamnan ya kuma jagoranci shanruwa a ranar Asabar daya ga watan Ramadan wanda gwamnatin Jihar Kano ta shirya.

Sauran bukukuwan sun hada da bikin hawan dabar da walimar cin abincin dare da kuma rangadi a wasu ayyuka da gwamnan ya yi ko yake kan yi.

Bikin cikar Kano shekara 50 na dada kara armashi

Gwamna Ganduje ya jagoranci tattaunawa tsakanin gwamnati da al’ummar gari

An kuma gudanar da liyafa ta musamman domin karrama yan mazan jiya da suka taka gagarumin rawa wajen kafuwar Kano.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, daga cikin iyalan yan mazan jiya da aka karrama a wajen liyafar sun hada da iyalan margayi shugaba Janar Murtala Mohammed da iyalan Janar Sani Abacha, na margayi Mallam Aminu Kano, da iyalan margayi Sarki Sanusi I, da na Sarki Ado Bayero da dai sauransu.

Gwamna Ganduje ya kuma karrama iyalan tsoffin gwamnonin jihar da suka hada da Audu Bako da Mallam Abubakar Rimi da Muhammad Abdullahi Wase da iyalan margayi Kanal Obukadata Oneya da sauransu.

Bikin ya kuma samu karrama iyalan Alhaji Aminu Dantata, da na Khalifa Sheikh Isiaku Rabiu, da na Danmasanin Kano, Dakta Yusuf Maitama Sule, da Alhaji Tanko Yakasai da dai sauransu.

Daga cikin manyan mutane da suka halarci tarurrukan da kuma hawan Dabar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, gwamnonin jihohin Zinder da Maradi daga jamhoriyar Niger.

KU KARANTA: An bawa mulkin Buhari karamin maki a cikarsa shekara 2

Sauran mashahuran da suka halarci bukukuwan sun hada da tsofaffin gwamnonin Kano da Sarakunan Jigawa.

Daraktan yada labarai da sadarwa na fadar gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakasai yace ana cigaba da gudanar da bukukuwan cikar Kano shekara 50 da kafuwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel