Kun ga sabon mai horas war da kungiyar Barcelona ta nada

Kun ga sabon mai horas war da kungiyar Barcelona ta nada

- A na sa ran a ranar Litinin kulob din Barcelona zai sanar da nadin Ernesto Valverde a matsayin sabon kocin kungiyar bayan tafiyar Luis Enrique.

- Tsohon dan wasan gaban Barca Valverde ya sanar a makon jiya cewa zai bar Athletic Bilbao bayan ya shafe shekara hudu yana jagorantar kungiyar.

Kocin mai shekara 53 zai maye gurbin Luis Enrique, wanda a watan Maris ya ce zai bar Barca a karshen kakar bana bayan ya yi shekara uku da su.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a wasan karshe da Enriqueya jagoranci Barcelona, kulob din ya doke Alaves da ci 3-1, inda hakan ya ba su damar daukar kofin Copa del Rey a ranar Asabar.

A ranar Litinin ne ake sa ran Shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu zai fitar da wata sanarwa kan batun.

Kun ga sabon mai horas war da kungiyar Barcelona ta nada

Kun ga sabon mai horas war da kungiyar Barcelona ta nada

Valverde ya yi wasa a Barcelona a tsakanin sheakarun 1988 zuwa 1990, inda ya ciyo mata kwallaye takwas a wasa 22 da ya buga.

Dan asalin kasar Spain, Valverde ya jagoranci Athletic Bilbao ta samu matsayi na bakwai a kakar La Ligar bana, yayin da Barcelona ta kare a mataki na biyu, Real Madrid kuma ta zama zakara.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel