Gwamnatin jihar Filato na shirin sake gina kasuwar Terminus

Gwamnatin jihar Filato na shirin sake gina kasuwar Terminus

- Gwamnatin jihar Filato ta nada kwamiti da zai gudanar da aikin gina babbar kasuwar Jos da aka fi sani da kasuwar Terminus, don habaka harkokin kasuwanci a jihar.

- Da yake zantawa da manema labarai a bikin ranar dimokaradiyya da cika shekaru biyu akan mulki, gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya ce suna da yakinin sake gina kasuwar ta Jos da ta kone shekaru 15 da suka gabata, wanda hakan zai inganta harkokin kasuwanci a jihar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a cewar gwamnan lokacin da suke yakin neman zabe sunyi alkawarin sake gina kasuwar, wanda hakan yasa yanzu suka samar da kwamitin da zasu gudanar da aikin. Haka kuma gwamnan yayi kira ga ‘yan kasuwa da su saka hannu domin taimakawa gwamnati.

Gwamnatin jihar Filato na shirin sake gina kasuwar Terminus

Gwamnatin jihar Filato na shirin sake gina kasuwar Terminus

Albarkacin ranar tunawa da dimokaradiyya gwamnan jihar Filato ya yiwa wasu firsinoni shida afuwa, kamar yadda Kwamishinan Shari’a a jihar Filato Jonathan Mawiyau, ya tabbatar.

Shugaban kungiyar kwararru a harkar yada labarai reshen jihar Filato, Nde Gideon Barde, ya shawarci gwamnatin jihar Filato da ta mayar da hankali ga kyautata aikin gona da kuma ilmi domin samun ci gaba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel