Jiga-jigan PDP sun bukaci Jonathan da kada ya tsayawa takarar shugaban kasa a 2019

Jiga-jigan PDP sun bukaci Jonathan da kada ya tsayawa takarar shugaban kasa a 2019

Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu ruwa da tsaki daga cikin jiga-jigan jam’iyyar adawa PDP sun fara matsa wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya jingine bukatar tsayawa takarar shugaban kasa a shekara ta 2019.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, jam’iyyar PDP ta na shirin sauya salon fafatawa da jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2019.

NAIJ.com ta samu labarin cewa majiyar ta ce, yayin da mafi yawan manyan jam’iyyar PDP ke bukatar Jonathan ya sake fitowa takara, wasu daga cikin su kuma na ganin babu wata hanyar da za a iya tallata Jonathan ga ‘yan Nijeriya a halin yanzu.

Jiga-jigan PDP sun bukaci Jonathan da kada ya tsayawa takarar shugaban kasa a 2019

Jiga-jigan PDP sun bukaci Jonathan da kada ya tsayawa takarar shugaban kasa a 2019

Sai dai wata kwakkwarar majiya daga jam’iyyar PDP ta shaida wa manema labarai cewa, duk da ya ke su na jiran hukuncin kotun koli dangane da shugabancin jam’iyyar, amma sun yi nisa a kan shirin su na tunkarar APC a zaben shekara ta 2019.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel