Anyi wa fursunoni 34 afuwa a wannan jihar ta Najeriya (Karanta)

Anyi wa fursunoni 34 afuwa a wannan jihar ta Najeriya (Karanta)

Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross River yayi afuwa ga fursunoni 34, dake zaman wakafi a gidan yarin Kalaba, a wani bangare na bikin cika Shekaru 50 da kirkiro jihar.

Mista Ayade ya bayyana haka ne ajiya Asabar a Kalaba, cikin jawabinsa na cikar jihar Shekaru 50, yace jihar tana da kwararan dalilai da zai sa tayi bikin murnar idan akayi duba da irin nasarorin da ta cimma cikin wadannan shekaru.

NAIJ.com ta samu labarin cewa yace anyi afuwan ne saboda bikin bisa dogaro da tanadin kundin tsarin mulki na shekarar 1999, sashi na 212.

Anyi wa fursunoni 34 afuwa a wannan jihar ta Najeriya (Karanta)

Anyi wa fursunoni 34 afuwa a wannan jihar ta Najeriya (Karanta)

Mista Ayade ya ja hankalin mutanen jihar da su rika tunawa da tsofaffin shugabannin jihar da suka bada gudunmawar su wajen ciyar da jihar gaba.

Yace duk da kalubalen da jihar take fuskanta akwai bukatar mutanen jihar su kasance masu fatan samun rayuwa mai kyau anan gaba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel