Wani mutumi ya yi yunkurin kashe kan shi saboda an hana shi takarar shugaban kasa

Wani mutumi ya yi yunkurin kashe kan shi saboda an hana shi takarar shugaban kasa

- Wani dan siyasa mai suna Peter Gichira a kasar Kenya ya yi yunkurin kashe kanshi

- Ya yi wannan yunkuri ne saboda hukumar zabe ta kasar ta hana shi tsayawa takarar shugabancin kasar

- Hukumar ta hana shi tsayawa ne saboda bai cika sharudan da aka gindaya na tsayawa takarar ba

Wani dan siyasa mai suna Peter Gichira a kasar Kenya ya yi yunkurin kashe kanshi a saboda hana shi fitowa takarar shugabancin kasa da hukumar zabe ta kasar ta yi.

Hukumar zaben kasar ta hana Peter da wasu manyan ‘yan siyasa 8 tsayawa takarar ne sakamakon gaza cika sharudan takarar da ba suyi ba, wanda ya hada da samun goyon bayan mutane 2,000 wadanda ba su da alaka da kowace jam’iyya kuma suka fito daga akalla jahohi 24 cikin 47 da kasar ke da su.

KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba – hukumar shirya gangamin zabe

Wani mutumi ya yi yunkurin kashe kan shi saboda an hana shi takarar shugaban kasa

Wani mutumi ya yi yunkurin kashe kan shi saboda an hana shi takarar shugaban kasa

‘Yan sanda sun kama Peter a ranar Asabar 27 ga watan Mayu a lokacin da yake yunkurin fadowa daga benen hukumar zaben kasar mai hawa shida.

Tuni dai a ka gurfanar da shi a gaban shari’a.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: Yadda wani Alaranma ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a daya

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kafin afkuwar wannan al'amari mai ban al'ajabi babu wanda ya san da wani mutum mai suna Peter Gichira.

Kasar dai za ta yi zaben ta na gaba ne a ranar 8 ga watan Agusta, inda ake kyautata zaton za a fafata tsakanin shugaban kasa mai ci wanda ke neman wa’adi na biyu, wato Uhuru Kenyata da kuma jagoran ‘yan adawar kasar, Raila Odinga, wanda ke takara a karo na hudu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo masu bidiyo kan tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da ya bayyana yadda za;a dunga kula da Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel