'Yan gudun hijira za su yi Sallan layya a gida — Shettima

'Yan gudun hijira za su yi Sallan layya a gida — Shettima

Gwamnatin jihar Borno ta yi alƙawarin cewa 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ta raba da muhallansu zasu iya komawa gidajen da aka sake ginamusu kafin karshen shekarar musulunci.

Kafin watan azumi, gwamnan jihar yayi musu alkawarin cewa zasu bar sansanin yan gudun hijra ne kafin karshen watan Mayu amma abin abi yiwu ba.

Gwamna Kashim Shettima ya bayyana cewa dalili shine har yanzu rundunar sojin Najeriya na cigaba da shara a dajin Sambisa. Kana kuma saboda a karasa gine-ginen makarantunsu, asbibitoci, rijiyan burtsatsai da sauran su.

Wasu jawabai da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun ce mutane fiye da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya tilastawa barin muhallansu a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Sanadiyar haka ya sanya suka koma zama a sansunan yan gudun hijra a jihohin daban- daban musamman garin Maiduguri.

'Yan gudun hijira za su yi Sallan layya a gida — Shettima

'Yan gudun hijira za su yi Sallan layya a gida — Shettima

Baya ga haka akwai 'yan gudun hijrar Nijeriya sama da dubu 450 da ke zaune a wasu sansanonin da ke ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi.

KU KARANTA: Dangote na shirin bude kamfanin sukari a arewa

Majalisar dinkin duniya tace:

"A garin Damasak kaɗai akwai mutum dubu 72, kuma mun gina garin har zuwa kashi saba'in da biyar cikin ɗari. Inda muka samu matsalaloli su ne garuruwan Bama da Gwoza ko da yake, an ci karfin aikin."

Duk da cewan akwai sauran aiki musamman wajen tabbatar da tsaron mutan da dukiyoyinsu, gwamnan jihar Borno ya bada tabbatacin cewa zasuyi duk abinda ake bukata domin tabbatar da cewa mutane sun koma muhalansu, yace:

"Na bayar da tabbacin cewa kwana talatin bayan azumi za mu mayar da su, mun yi imani mutane za su yi sallar layya a garuruwansu."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel