Biafra: Hukumar yan sanda tayi gargadi ga yan kungiyar IPOB

Biafra: Hukumar yan sanda tayi gargadi ga yan kungiyar IPOB

Hukumar yan sandan jihar Enugu da Anambra tayi gargadi da masu yakin neman yancin Biafra akan wani abu da suke shirin yin a hana mutane ftowa daga gidajensu a yau 30 ga watan Mayu bisa ga umurnin kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB).

Ofishishin yan sandan sunyi wannan gargadi ne a jawabai daban-daban ranan Litinin.

Kwamishanan yan sandan jihar Anambra, Samuel Okaula, ya bayyanawa manema labarai cewa yan sanda na shirye da yaki da duk wanda zai saba doka.

Biafra: Hukumar yan sanda tayi gargadi ga yan kungiyar IPOB

Biafra: Hukumar yan sanda tayi gargadi ga yan kungiyar IPOB

Yace: “Ai dama muna shirye da irin wadannan abubuwa kuma muna jaddada cewa muna son mutanen jihar su fita sufurinsu nay au da kullum.

“Babu wani abin tashin hankali kuma ina tabbatar muku da cewa muna ankare da komai. Muna da jami’ai isassu kuma mun turasu wajaje daban-daban.

“Ban tunanin wani zai hana mutane fita yin ayyukansu nay au da kullum. Ba zan amince da wani yayi dauki doka a hannunsa ba. Duk wanda yayi hakan zai fuskanci fushin shari’a", Okaula yace.

KU KARANTA: An damke direban da ya arce da dukiyan N6m

Kwamishanan yace hukumar na shirye da tabbatar da tsaro kuma tabbatar da cewa jihar ce mafi zama lafiya a kasa.

Su kuma ofishin yan sandan jihar Enugu sun baiwa jama’a shawaran cewa kowa yafita ayyukanshi kada ya saurari wani zancen rashin fita.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel