Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba – hukumar shirya gangamin zabe

Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba – hukumar shirya gangamin zabe

- Kungiyar dake shirya gangamin Buhari ta bayyana cewa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari bai nemi zabe karo na biyu a 2019 ba, Najeriya za ta halaka

- Ta ce shekaru biyu da gwamnatin APC ta yi tana mulki ta yi matukar tasiri ga ‘yan Najeriya fiye da shekaru 16 da jam’iyyar PDP ta yi tana mulki

- Kungiyar ta kuma shirya tawagar malamai da fastoci don yima shugaba Buhari addu’an samun lafiya

Kungiyar dake shirya gangamin Buhari ta bayyana cewa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari bai nemi zabe karo na biyu a 2019 ba, Najeriya za ta rushe.

Kungiyar ta ce shekaru biyu da gwamnatin APC ta yi tana mulki ta yi matukar tasiri ga ‘yan Najeriya fiye da shekaru 16 da jam’iyyar PDP ta yi tana mulki.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kungiyar ta hada kimanin Limamai 14 da kuma fastoci shidda, ta yi addu’a na musamman domin samun lafiyar Buhari sannan kuma ta nuna yakinin cewa za’a ji dadi fiye da yanzu a shekaru biyu da suka rage ma gwamnatin.

Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba – hukumar shirya gangamin zabe

Kungiyar dake shirya gangamin zabe na Buhari ta ce Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba

A jiya Litinin, 29 ga watan Mayu da yake magana da manema labarai a hedkwatar kungiyar gangamin Buhari (BCO) a Abuja, shugaban kungiyar, Alhaji Danladi Pasali, ya ce a cikin shekaru biyu da Buhari ya yi a kan mulki ya shimfida tubulin mulki mai kyau a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Duk laifin ku ne: Ai ba ku taimaki Buhari ba Inji Ngige ga Inyamurai

Ya yi bayanin cewa idan Buhari ba tsaya takara a 2019 ba, fusatattun soji zasu karbe sannan sun hallaka kasar.

“Fitowar sa ta biyu a 2019 na da muhimmanci don ceto Najeriya. Har sai dai idan ya dawo a 2019, kasar nan zata halaka; sannan kuma zamu iya baku tabbacin cewa shugaban kasa zai kuma tsayawa takara. Kungiyar BCO na alfahari da ci gaba da aka kawo zuwa yanzu ta fannin tsaro, ci gaban tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa,” cewar sa.

‎ Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ba gwamnati goyon baya domin ta cimma nasararta ta fannin gina zaman lafiya da damokradiyya a kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Jama'a sun yi na'am da juyin mulki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel