Duk laifin ku ne: Ai ba ku taimaki Buhari ba Inji Ngige ga Inyamurai

Duk laifin ku ne: Ai ba ku taimaki Buhari ba Inji Ngige ga Inyamurai

– Inyamurai suna ta kokawa cewa ana murkushe su a Gwamnatin Buhari

– Jiya mu ka ji cewa Tsohon Gwamnan Jihar Imo Ikedi Ohakim ya kara fadin haka

– Wani Ministan Buhari ya maida masu martani

A cewar Chris Ngige Inyamurai ba su taimakawa Shugaba Buhari da komai ba.

Don haka yace su daina kukar cewa ba a tafiya da su a mulkin sa.

Inyamurai ba su ci kashi ba suna kokarin aman tsoka Inje Ngige

Duk laifin ku ne: Ai ba ku taimaki Buhari ba Inji Ngige ga Inyamurai

Ngige ya fadi zaben 2015 karkashin APC

Ministan kwadago Chris Ngige ya soki ‘Yan uwan sa Inyamurai da ke zargin Gwamnatin Shugaba Buhari su na cewa an ware su gefe. Ngige yace a lokacin yakin neman zabe sam Inyamurai ba su taimakawa Buhari ba.

KU KARANTA: Babu abin a zo-a gani tun da Buhari ya hau-Inji PDP

Duk laifin ku ne: Ai ba ku taimaki Buhari ba Inji Ngige ga Inyamurai

Abin ya isa haka: Inyamurai sun koka a harkar sha’anin siyasa

Ministan wanda ya fito daga Jihar Anambra ya kira Inyamurai su tashi tsaye su kuma shiryawa zaben 2019 da kyau. Ngige ya kira su cewa su guji yin irin abin da su kayi a 2015 inda su ka zabi Jam’iyyar PDP sak.

Jiya kun ji cewa Tsohon Gwamnan Jihar Imo Ikedi Ohakim yace dole ayi sauyi a harkar siyasar kasar domin kuwa ana murkushe kabilar Ibo. Ohakim yayi wannan kira ne a wani taro da aka yi a dakin taro na Chinue Achebe a Garin Nsukka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Jama'a sun yi na'am da juyin mulki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel