Dangote zai bude wani makeken kamfanin sukari a Najeriya

Dangote zai bude wani makeken kamfanin sukari a Najeriya

– Dangote na shirin bude wani katafaren kamfanin sukari a kasar nan

– Kamfanin zai ci fili har shekta 60,000 a Jihar Nasarawa

– Dubunnan Jama’a dai za su samu aikin yi

Attajirin Duniyar nan Dangote zai bude wani kamfani a Jihar Nasarawa.

Za a kashe sama da Naira Biliyan 217 wajen kamfanin na sukari.

A dai shekarar nan za a kammala wannan aiki.

Dangote zai bude wani makeken kamfanin sukari a Najeriya

Dangote zai bude wani babban kamfani a Arewa

Ana sa rai shekarar nan a kammala aikin kamfanin sukarin da Aliko Dangote yake yi a Jihar Nasarawa kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust. Za a kashe Biliyan 217 wajen gina kamfanin da zai ci fiye da shekta 60,000.

KU KARANTA: Dangote da El-Rufai da Sen. Bagudu za su saye kamfanin PAN

Dangote zai bude wani makeken kamfanin sukari a Najeriya

Wani makeken kamfanin Dangote a Najeriya

Sama da mutane 30,000 za su samu aikin yi ta sanadiyar kamfanin yayin da za a rika samun fiye da ton 30,000 na sukari a kowane shekara wanda wannan zai kawowa Najeriya sauki matuka. Jihar kan ta dai za ta samu lantarki a sanadiyar aikin.

Duk Nahiyar Afrika dai babu attajiri irin Alhaji Aliko Dangote. Jiya ne ma ku ka ji cewa Alhaji Aliko Dangote da wasu Gwamnoni biyu sun shirya sayen kamfanin PAN masu kera motocin Peugeot a Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abubuwa sun yi tsada a Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel