Shekaru 2 a mulki: Masana sun yabawa kokarin Shugaba Buhari

Shekaru 2 a mulki: Masana sun yabawa kokarin Shugaba Buhari

– Gwamnatin Shugaba Buhari ta shekara biyu da kafuwa

– Kungiyar ACF ta Arewa ta yaba da kokarin Gwamnatin

– An yabawa Shugaban kasar wajen sha’anin tsaro da yaki da barna

Shugaba Buhari

An yabawa Gwamnatin Shugaba Buhari

Kungiyar ACF ta yabawa Shugaba Buhari wajen harkar tsaro.

Masana sun ce akwai bukatar a gyara hanyoyi a Najeriya.

An kira Shugaban kasar ya zage dantse wajen harkar tattalin arziki.

Kungiyar ACF ta manyan Arewa ta yabawa Gwamnatin Shugaba Buhari yayin da ta cika shekaru 2 da kafuwa. A cewar Kungiyar Shugaban kasar yayi kokari wajen yaki da ta’addanci da kuma tsagera. An kuma yabawa Shugaban kasar wajen yakar sata da ya dauko gadan-gadan.

KU KARANTA: Buhari bai yi kokari ba Inji wani Dan APC

Shugaba Buhari

Shugaban kasa yayi kokari wajen yaki da ta’addanci

Masana siyasa sun ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta gina tituna da sauran abubuwan more rayuwa. Har wa yau kuma an yabawa tsarin nan na daukar matasa aiki watau N-Power na Gwamnatin. Kungiyar tace akwai kuma bukatar a dage wajen gyara tattalin arzikin kasar.

Mai magana da bakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Garba Shehu ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta ware sama da Naira Biliyan 54 domin biyan tsofaffin ma’aikata kudin su na fansho.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani yayi da'awar cewa Shugaba Buhari ya mutu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel