Bayan takaddama tsakanin majalisa da fadar shugaban kasa gaskiya ta yi halinta – Inji wani dan majalisa

Bayan takaddama tsakanin majalisa da fadar shugaban kasa gaskiya ta yi halinta – Inji wani dan majalisa

- Majalisar dattawa tace ta ba gwamnatin shugaba Buhari goyon baya ka kan yaki da cin hanci da rashawa

- Sanata Aliyu Sabe Abdullahi ya ce majalisar dattawance ta bada goyon bayan gwamnati ta samar da asusun ajiya na banki guda daya

- Sanata Ibrahim Musa ya ce dama rashin fahimta yasa ake ganin kamar sanatocin na kokarin takawa Buhari Burki

Majalisar dattawa ta ce ta ba fadar shugaban kasar goyon baya dari bisa dari a kan yaki da cin hanci da rashawa a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban kwamitin labarai na majalisar Sanata Aliyu Sabe Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a Minna, ya ce hasali ma, majalisar dattawance ta bada goyon bayan gwamnati ta samar da asusun ajiya na banki guda daya da hakan yasa lamarin ya yi tasiri.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, sanata Ibrahim Musa, ya ce dama rashin fahimta yasa ake ganin kamar sanatocin na kokarin takawa shugaba Muhammadu Buhari Burki.

Bayan takaddama tsakanin majalisa da fadar shugaban kasa gaskiya ta yi halinta – Ini wai dan malisa

Majalisar dattawan Najeriya

Shima dan majalisar wakilan Najeriya, Hon Abubakar Lado Suleja, ya ce bayan takaddamar da aka yi ta samu tsakanin ‘yan majalisar da fadar shugaban kasa, daga bisani gaskiya ta yi halinta.

KU KARANTA: Dangantakar dake tskanina da gwamna Tambuwal – Obasanjo

Da hukumomi a matakai daban daban ke jawabi albarkacin zagayowar ranar mulkin farar hula a Najeriya, dan majalisar wakilai Abdullahi Idris Garba, ya bayyana cewa ya taimakawa matasa daga yankinsa da kayan koyon sana’o’i na sama da miliyan 80 domin rage zaman banza a tsakanin matasan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Femi Fani Kayode ya bayyana cikakken bayani da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel