Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya kan shugabancin Buhari

Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya kan shugabancin Buhari

- Wasu ‘yan Najeriya na tofa albarkacin bakinsu game da shugabancin kasar nan a karkashin jagorancin jam’iyyar mai mulki APC

- Wasu na ganin cewa an sami ci gaba a wasu bangaren musamman harkar tsaro

- ‘Yan Najeriya sun gargadi gwamnati da ta karbi shawarwarin da ake gabatar ma ta

Yayin da gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin shugaba Mohammadu Buhari ta jam’iyyar APC ke cika shekaru biyu kan mulki, ‘yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkancin bakinsu game da rawar da gwamnatin ta taka a shekaru biyu da suka gabata.

A lokacin da wasu ‘yan Najeriyar ke ganin an sami ci gaba a wasu bangaren, ta wasu bangaren kuma abin ba haka yake ba musamman idan aka duba harkar tsaro akwai ci gaba sosai.

Sai dai kuma a yayin da wasu ke ganin an ci gaba, wasu kuma na kushewa tare da bayar da shawarwarin ta yarda za a kawo karshen matsalolin da gwamnatin ta gada daga gwamnatin da ta shude.

Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya kan shugabancin Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawa sanata Bukola Saraki a fadar gwamnati

KU KARANTA: Madallah! An gudanar da addu'o'i na musamman ga Buhari a wannan jihar ta Arewa

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, wasu kuma na ganin cewa a halin da ake ciki yanzu zai yi wahala a samu mutumin da zai iya fadawa shugaba Buhari gaskiyar halin da ake ciki a Najeriya.

Fatan ‘yan Najeriya dai shine ganin gwamnati ta karbi shawarwarin da ake gabatar ma ta, na jan damara domin tunkarar matsalolin da ke gaba kafin zaben shekara 2019.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan ko mata za su iya shugabancin kasar nan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel