‘Yan Biyafara sun zargi Rundunar Soji da yi masu ruwan wuta

‘Yan Biyafara sun zargi Rundunar Soji da yi masu ruwan wuta

– Rundunar Sojin Najeriya sun yi ya ‘Yan Biyafara ruwan wuta

– Mai magana da bakin Kungiyar IPOB ya bayyana haka

– Kungiyar IPOB ta zargi Sojojin Najeriya da hallaka Jama’ar ta

An zargi Sojojin Najeriya da yi wa mutanen ta aman wuta.

Emma Powerful ya zargi Jami’an tsaro da kokarin ganin bayan Jama’ar su.

Ana kokarin bikin tunawa da Ranar Biyafara.

‘Yan Biyafara sun zargi Rundunar Soji da yi masu ruwan wuta

Sojoji sun yi wa mutanen Biyafara luguden wuta Inji IPOB

Yayin da Jama'an Yankin Biyafara ke kokarin tunawa da mutanen su da su ka kwanta dama a lokacin Yakin Basasa, Sojojin Najeriya sun budawa mutanen nan Biyafara wuta a Garin Aba da ke Jihar Abia.

KU KARANTA: Sojoji sun fasa garken 'Yan Boko Haram

‘Yan Biyafara sun zargi Rundunar Soji da yi masu ruwan wuta

Rundunar Sojin Najeriya a Garin Kuros-Riba

Kakakin Kungiyar IPOB mai fafutukar neman kasar Biyafara Emma Powerful ya bayyana haka. Emma ya zargi Sojojin da ya kira na Hausa-Fulani da kokarin ganin bayan Jama’ar su inda yace an yi masu aman harsashi ta sama da kasa.

Kwanakin baya matan Kungiyar IPOB na Biyafara su ke cewa an kai masu hari yayin da su ke wata zanga-zanga domin tunawa da mutanen su da aka kashe. Kanal Sagir Musa wanda shi ne na biyu wajen harkar yada labarai a gidan Soji ya musanya zargin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Jama'a na goyon bayan Mulkin Soji ? [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel