Gwamnatin Tarayya na shirin rufe iyakokin kasa, ko me yayi zafi?

Gwamnatin Tarayya na shirin rufe iyakokin kasa, ko me yayi zafi?

- Gwamnatin Tarayya na barazanar rufe iyakokin ta da kasa

- Har yanzu ana sumogar shinkafa da sauran haramtattun kaya

- Kudirin Gwamnati ne a noma abun da za'a ci har ma a sayar a kasashen waje, ba wai a ci gaba da shigo dasu ba

A kokarinta na ganin an wadata da kayan abinci, an koma dogaro da kai a kasa, an kuma sami wadatar abinci da habaka tattalin arziki, Gwamnatin Tarayya a baya ta hana shigo da wasu kaya wadanda za'a iya samar dasu a cikin kasa, ciki ko harda abincin da aka fi ci a kasar, da ma duniya baki-daya, wato shinkafa.

Sai dai hakan na fuskantar kalu-bale iri-iri, daga rashin kudi ga manoma, da rashin ilmin noma na zamani, hada da sumoga inda ake shigo da kayan abincin ta iyakoki a boye Gwamnati dai na iya kokarin ta hana hakan, amma abin ya faskara.

A yanzu dai tace muddin hakan ya ci gaba, to fa zama a rufe iyakokin baki daya kowa ya huta.

KU KARANTA KUMA: An bawa mulkin Buhari karamin maki a cikarsa shekara 2

Gwamnatin Tarayya na shirin rufe iyakokin kasa, ko me yayi zafi?

Gwamnatin Tarayya na shirin rufe iyakokin kasa, ko me yayi zafi?

NAIJ.com ta tattaro cewa Ministan Noma na kasa Audu Ogbeh ne yayi wannan furuci, inda yake tsokaci a yau da safen nan, yace muddi basu daina tadiye kafar gwamnati ba wajen gurgunta tattalin arziki, mu kuma baza muyi kasa a gwiwa ba wajen koya wa masu tu'annati hankali, domin ba gudu ba ja da baya so muke a 2018, Najeriya ta zama tana iya samarwa da kanta abinci wadatacce.

Ya kara da cewa, yarjejeniyar ECOWAS da kasashen yammacin Afirka shine barin boda a bude, amma hakan baya nufin ayi amfani da wannan damar don makota kasashe su zama hanyar gurgunta wata kasar, kuma duk da Najeriya uwa ce a yankin, hakan baya nufin ta kar kanta don farantawa makwabta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel